GASKIYA TA FI KWABO   (Kaduna, Nigeria)  Alhamis, 29 ga Agusta, 1991 shafi na goma sha biyu
 
Wani Furofesa Daga Japan Ya Kawo Ziyara Ofishin Gaskiya
 

daga Balarabe Ladan Lemu, Kaduna



 
    An bayyana harshen Hausa da cewa, harshe ne mai babban matsayi a duniya, domin kuwa a nahiyar Afirka bake d'ayanta in ban da harshen Larabci babu harshen da ya kai shi yawan Jama'a masu amfani da shi.

    Malam Yahaya 'Danjuma (Mr. John Philips), wani Bature Ba'amirke mai sha'awar harshen Hausa wanda ya zo daga k'asar Japan ne ya yi wannan bayanin a lokacin da ya kawo ziyara ofishin Gaskiya Ta Fi Kwabo ranar Litinin d'in da ta gabata.
 
    Ya ci gaba da bayyana cewa harshen Hausa na d'aya daga cikin manyan harsuna guda uku a najiyar Afirka, domin kuwa daga Larabci sai Hausa sai kuma Suwahili, in aka yi la'akari da yawan Jama'ar da suke yin amfani da harsunan.

    Malam Yahaya, wanda Malamin Harshen Turanci ne a Jami'ar koyon tattalin arziki da kuma fannin shari'a da ke Akita a k'asar Japan, ya ce ya zo k'asar Hausa ne domin ci gaba da gudanar da bincike a kan tarihin k'asar Hausa a k'arni na 20 watau zamanin mulkin Turawa.

    Ya ce ya koyi harshen Hausa ne a Jami'ar California da ke k'asar Amirka, a wurin Malam Takalmi (Shuh), domin ya ji dad'in gudanar da binciken nasa.

    Malam Yahaya ya ce a lokacin da suke koyon harshen Hausa a can Jami'ar ta California, Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo na cikin abubuwan da suke yin amfani da su wajen koyon harshen.

    Ya bayyana cewa yana sha'awar da yawa daga cikin al'adun Hausawa musamman halin nan nasu na kunya da karb'ar bak'i hannu bibbiyu da tufafinsu da abincinsu, kamar su d'an wake da tuwon dawa da miyar kuka ko miyar kuka ko miyar kub'ewa da goro, wad'anda ya ce duk d'and'ana su kuma ya ji dad'insu sosai.

    Malamin ya ce ya tab'a zuwa nan k'asar Hausa domin gudanar da bincike a kan tarihin k'asar Hausa domin gudanar da bincike a kan tarihin k'asar Hausa a k'arni na 19 lokacin da ya yi watanni har goma sha d'aya a nan.

    Ya nuna takaicin ganin, cewa babu sashin Hausa a Rediyon Tokyo da kuma ta Faransa duk da cewa akwai Malami guda d'aya na harshen Hausa a can Jami'ar Koyon Harsunan K'asashen Waje d'in da ke Tokyo.

    Malam Yahaya ya bayyana, cewa akwai wad'ansu kamannu a tsakanin harsunan Hausa da Japananci, musamman wajen furta haruffan 'ph' da kuma 'f'.

    Daga k'arshe, ya jinjina wa al'ummar Afirka dangane da yadda suke da saurin fahimtar wad'ansu harsuna da ba nasu ba fiye da wad'ansu jinsin mutane na k'asashen duniya.
 

 



 
back to essays
 
back to homepage